An kai harin Bom a Kano
Akalla mutane biyar aka ruwaito sun mutu, Takwas kuma suka jikkata a wani harin bom da aka kai a wani wajen da Kiristoci ke ibada a garin Kano. Wasu Rahotanni daga Kano sun ce wani bom ya tashi da wata Mata da ta je dasa bom din a kofar Nasarawa, a daidai lokacin da Al'ummar Najeriya ke bikin Sallah bayan kammala Azumin Ramadan.
Wallafawa ranar:
Wakilin RFI Hausa a Kano Abubakar Issa Dandago yace an kai harin ne a kan titin Zungeru a unguwar Sabon gari.
Kakakin rundunar ‘Yan Sanda Frank Mba yace an jefa bom din ne a kan hanya, a harabar Mujami’ar mabiya darikar Katolika, inda Mayakan Boko Haram suka taba kai hari.
Wannan harin na zuwa ne duka sa’o’I biyu, bayan an kai wani harin bom a unguwar Nasarawa a garin Kano, amma Dandago yace harin bai shafi kowa ba.
A Jajibirin Sallah rundunar 'Yan sanda tace ta yi nasarar kwance wasu bama bamai da aka dasa a cikin wata Mota kirar Peugeot a kusa da Masallacin Isyaka Rabi'u.
Yanzu haka ‘Yan sanda sun cafke mutane uku da ake zargin sun kai hare haren a yau Lahadi da musulmi ke bikin Sallah.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu