Isa ga babban shafi
Afrika

An kafa rundunar Tafkin Chadi don yaki da Boko Haram

Kasashe hudu mambobin kungiyar raya tafkin Chadi sun kafa wata rundunar sojan dakarun hadin guiwa da zata yi yaki da Mayakan kungiyar Boko Haram na Najeriya, kamar yadda majiyar hukumomin kasashen ta tabbatar.

'Yan gudun hijira daga Najeriya a yankin Kamaru
'Yan gudun hijira daga Najeriya a yankin Kamaru AFP PHOTO / REINNIER KAZE
Talla

Wata Majiyar zaman taron shuwagabannin rundunonin Sojan kasashen Niajr da Najeriya da Chadi da Kamaru da suka gudanar a birnin Yamai na kasar Jamhuriyar Nijar, kasashen sun cim ma yarjejeniyar kafa rundunar sojan da zata kunshi dakaru 700 don yin gwagwarmaya da kungiyar Boko Haram a Tarayyar Najeriya.

A farkon watan Mayun daya gabata Shuwagabannin kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da Benin, tare da Faransa suka amince da wani shirin yaki da mayakan kungiyoyin da ke fada da sunan musulunci a nahiyar Afrika, tare da amincewa a kafa rundunar da ya kamata a girka a yankin tafkin Chadi, mai karfin kai dauki idan bukatar hakan ta tashi

Tuni dai Kasar Faransa da ke da niyar kafa rundunar da ke kunshe da dakaru 3000 domin yaki da mayakan islama a yankin Sahel, ta yaba da matakin da kasashen dangane da kafa wannan runduna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.