Isa ga babban shafi
Najeriya

Mayakan Boko Haram sun kashe mutane da dama a Gwoza

Mayakan Kungiyar Boko Haram a Najeriya sun kashe mutane da dama bayan sun kadddmar da mummunan hari a garin Gwoza da ke cikin Jihar Borno. Bayanai sun ce Mayakan sun kai wa Jami’an tsaro hari ne sanye da kakin soja kafin su abka wa garin inda suka yi ta kona gidaje da wuraren ibada.

Familles de Gwoza, dans l'Etat de Brono, déplacées par la guerre contre Boko Haram, en février 2014.
Familles de Gwoza, dans l'Etat de Brono, déplacées par la guerre contre Boko Haram, en février 2014. REUTERS/stringer
Talla

Wasu da suka tsira daga harin sun shaidawa RFI Hausa cewa halin da ake ciki a garin ya kazance domin mutane da dama sun fice daga Gwoza.

Wani Mazaunin Gwoza mai suna James Mshelia ya shaidawa Kamfanin dillacin labaran Faransa cewa maharan sun yi wa mutane da dama yankan rago tare da kona Ofishin ‘Yan sanda.

Mazauna garin Gwoza sun ce babu wani Jami’in tsaro da ya kawo dauki a garin a lokacin da Mayakan suka kaddamar da hari, yayin da kuma Rahotanni ke cewa an sace Hakimin garin Mohammed Idrisssa Timta wanda ya gaji mahaifinsa da Mayakan Boko Haram suka kashe a watan Mayu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.