Isa ga babban shafi
Kamaru

‘Yan bindiga sun kashe mutane 10 a Kamaru

‘Yan Sanda a Kamaru sun ce wasu ‘Yan bindiga da ake zargin Mayakan Boko Haram ne sun kashe mutane 10 a wani hari da suka kai a arewacin kasar kusa da kan iyaka da Najeriya.

Mayakan Boko Haram, tare da shugabansu Abubakar Shekau
Mayakan Boko Haram, tare da shugabansu Abubakar Shekau AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

‘Yan bindigar sun kai harin ne a Zigague kuma Wani Jami’in ‘Yan sanda ya shaidawa Kamfanin Dillacin Labaran Faransa cewa ‘Yan bindigar sun rufe babbar hanya ne a yankin tare da budewa Fasinjan wata mota kirar bus wuta.

Jami’in ‘Yan sanda yace Fasinja 9 da direbansu da ke cikin motar ‘Yan bindigar suka kashe tare da harbe wani Soja da ke cikin motarsa.

Kafar Rediyo mallakin gwamnatin Kamaru ta daura alhakin haring a Mayakan Boko Haram

Wannan na zuwa ne kwanaki bayan shugaba Paul Biya ya nada sabon kwamanda a Yankin don yaki da Boko Haram bayan sun kai hari a Kolafata a kwanan baya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.