Isa ga babban shafi
Nijar

Magajin garin Damagaram ya tsallaka rijiya ta baya

Magajin garin Damagaram ya yi nasarar tsallake wani yunkurin tube shi daga kan mukaminsa da wasu ‘yan Majalisar birnin suka yi a jiya litinin bisa zargin gazawa wajen tafiyar da ayyukan da suka rataya a wuyansa.

Fadar Sarkin Damagaram a Jmhuriyar Nijar
Fadar Sarkin Damagaram a Jmhuriyar Nijar Talatu/Carmen
Talla

Magajin garin Bashir Sabo, ya samu kuri’u 19 daga cikin 23 yayin da masu adawa da shi suka samu kuri’u 4 bayan kammala jefa kuri’a dangane da wannan yunkuri.

Da dai wasu ‘yan majalisar birnin na Damagaram 8 ne karkashin jagorancin mataimakin magajin garin Abdoulrahim Balarabe suka sanya hannu kan bukatar neman tube Bashir Sabo daga mukaminsa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.