Isa ga babban shafi
Kungiyar Tarayyar Turai

Kayayaki China na barazana a kasashen turai-Rahoto

Hukumar da ke sa’ido akan inganci kayayaki Turai ta gargadi cewa akasari kayayaki da ake shigowa da su daga kasashen su musamma na kasar china na tattare da babba hatsari, lamari dake barazana ga al’ummah kasashen

Tutocin Kasashen Turai
Tutocin Kasashen Turai
Talla

A wani rahotan da Hukumar ta fitar, ta ce a cikin shekarar da ta gabata akalla ta sanar da samun kayyaki da basu da inganci sau 2,435 wadanda akasarin su kayayki wasan yara ne, da sarkokin da mata ke amfani dasu wajen ado, takalma, da kayan sawa, adaddin daya haura na shekarar 2013 da kaso 3

Hukumar ta kuma bayyana cewa kashi 66 cikin 100 na kayayaki masu haddari ana shigowa da su ne daga kasar china wato sin , da kuma Hong Kong

Kuma ana samun kayayaki ne a kasashen turai 28 wadanda suka hadda da Norway, Iceland da Liechtenstein

Kwamishina kungiyar tarayya turai mai kula da kuma kare wadanda ke siyan kaya domin amfani dasu, Vera Jourova ta gargadi Iyayye dasu san irin kayayaki wasannin da za su ke siyawa ya’yansu.

Jourova ta kuma koka akan yadda ake samu yawan adaddin shigowa da kayayakin masu hatsari a kasashen turai, inda tace kungiyar kasashen turai zata gudanar da zaman fahimta da kasar china domin jadada mata kayayaki daya kamata ake shigowa da su kasashen su
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.