Isa ga babban shafi
Faransa

Gwajin jini domin gano wanda ya aikata fyade a Faransa

Sama da dalibai 500 ne maza da malamansu a wata makarantar Faransa aka kaddamar da gwajin jininsu domin gano wanda ya yi wa wata yarinya fyade mai shekaru 16 a cikin ban-daki. Masu gabatar da kara sun ce duk dalibin da kauracewa gwajin jinin, zai kasance mutum na farko da za’a tuhuma.

Harabar makarantar lycée Fenelon Notre-Dame a garin La Rochelle.
Harabar makarantar lycée Fenelon Notre-Dame a garin La Rochelle. AFP PHOTO / XAVIER LEOTY
Talla

Tun da sanyin safiya ne aka fara gudanar da gwajin daliban a lokacin da suka shiga aji a makarantar Fenelon-Notre Dame wata makaranta mai zaman kanta ta mujami’ar Katolika a yankin kudu maso gabacin La roshel (La Rochelle). Domin gano wanda ya yi wa yarinya mai shekaru 16 fyade a cikin makewayi ko ban daki.

Kuma za’a ci gaba da aikin gwajin jinin daliban da suka kai 475 da malamansu 31 har uzwa ranar Laraba domin gano wanda ya yi wa Yarinyar fyade
A ranar 30 ga watan Satumba ne aka yi wa yarinyar fyaden kuma a lokacin wanda ya aikata mummunan aikin ya kashe wuta a cikin ban dakin wanda hakan kuma yarinyar ba zata iya gane fuskanr shi ba.

Amma masu bincike zasu iya gano wanda ya aikawa yariyar fyaden ta hanyar gwaji daga abinciken da suka gudanar a kayan da ke jikin yarinyar.

Sai dai kuma wasu suna ganin hakan ya keta hakkin mutanen, amma mahukuntan da ke binciken sun ce zasu aiwatar da bincike ne tare da amintar iyayen yaran. Kuma daliban dukkaninsu sun amince a aiwatar da gwajin domin zakulo wanda ya yi wa yariyar fyade.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.