Labarun karshe
Rasha - 
Wallafa labari : Alhamis 13 Disamba 2012 - Bugawa ta karshe : Alhamis 13 Disamba 2012

Putin ya nemi ‘Yan adawa su kauce wa kutsen da Turawa ke yi a siyasar Rasha

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin
REUTERS/Grigory Dukor

Daga Awwal Ahmad Janyau / Bashir Ibrahim Idris

Shugaban Kasar Rasha, Vladimir Putin, ya soki ‘Yan adawar kasar da ke karbar kudade daga kasashen waje don haifar da rudani, inda ya ke cewa ba za su bari kasashen Turai su tilasta wa kasar Dimokuradiyya ba.

Yayin da ya ke jawabin sa na farko ga Yan kasar, tun dawowar sa karagar mulki, shugaba Putin ya bukaci al’ummar kasar da su kara yawan haihuwan yara, don kara yawan al’ummar kasar.

Shugaban ya kuma bukaci Majalisar kasa ta yi dokar hana ‘Yan kasar mallakar asusun ajiya a kasashen waje.

tags: Rasha - Vladimir Putin
KAN MAUDU'I GUDA
Ra'ayoyi
Bada ra'ayi kan wannan magana
The content of this field is kept private and will not be shown publicly.
To prevent automated spam submissions leave this field empty.
CAPTCHA
This question is for testing whether you are a human visitor and to prevent automated spam submissions.
Close