Isa ga babban shafi
Nigeria

‘Yan Bindiga sun sace Sarkin Dankon Bukkuyum a jihar Zamfara

Wasu ‘yan Bindiga dadi da ba’a kai ga tantance ko su waye ba a Najeriya, sun sace Sarkin Dankon Bukkuyum a jihar Zamfara Alhaji Muhammadu Usman

Taswirar Jahar Zamfara a Najeriya
Taswirar Jahar Zamfara a Najeriya
Talla

Wata majiya mai tushe ta tabbatar mana da cewar maharani sun zo ne a cikin wata Mota kirar Hilox dauke da hatsabiban Bindigogi a Hannayensu, suka kuma afkawa Sarki bayan fitowa Masallaci da Magariba kamin sallar Isha’i.

Wani shaidun gani da Ido kuma mai suna Abdullahi Muhammad ya ce sai da maharani suka sa kowa ya kwanta a bakin masallacin, ciki hadda shi mai bamu labarin, kamin daga bisani suka saka Mai martaba Sarki a mota da karfin tsiya, bayan da ya ki amincewa ya shiga Mota kuma suka yi gaba da shi.

Ya zuwa yanzu dai Rundunar ‘Yan sanda ta jihar Zamfara ba tace komai akai ba, amma wata kwakkwarar majiyar jami’an tsaro ta ce yanzu haka akwai wani aikin sirri da suke akan wannan hatsari.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.