Isa ga babban shafi

A kullum mutane 28 ake kashewa da kuma yin garkuwa da 24 a Najeriya - Rahoto

Akalla mutane dubu dubu 2 da dari 583 ne aka kashe sannan aka yi garkuwa da wasu 2 da 164 a zangon farko na wannan shekarar a Najeriya.

Yadda Jaridar Daily Trust ta zana yankunan da matsalar tsaro ta fi kamari a zangon farkon wannan shekarar.
Yadda Jaridar Daily Trust ta zana yankunan da matsalar tsaro ta fi kamari a zangon farkon wannan shekarar. © Daily Trust
Talla

Alkaluman dai na kunshe ne a cikin rahoton da kamfanin tsaro na Beacon Security and Intelligence Limited, masu bincike kan halin da tsaro ke ciki a Najeriya ya fitar.

Rahoton ya nuna cewar adadin mutanen da ake kashewa a kowace rana ya zarce adadin wanda ake yin garkuwa da su a kasar daga tsakanin watan Janairu zuwa Maris.

Ya kuma ce kashi 80 cikin dari na wadanda aka kashe da kuma kashi 94 na wadanda aka yi garkuwa da su, daga Arewacin kasar suka fito.

Rahoton ya nuna cewar akalla mutane 28 ake kashewa a Najeriya da kuma yin garkuwa da 24 a kowa ce rana.

Yankunan da matsalar tafi kamari

A cewar alkaluman da Kamfanin na Beacon ya fitar, daga cikin mutanen da aka kashe a tsakanin watannin Janairu zuwa Maris, sanadiyar hare-haren ‘yan bindiga da rikicin manoma da makiya da kuma na kabilanci, adadin wadanda suka mutu a yankin Arewacin Najeriya ne yafi yawa, inda a shiyar Arewa maso Yamma mutane dari 793 suka mutu, a shiyar Arewa maso Gabas mutane 681, a shiyar Arewa ta Tsakiya kuma akwai mutane 596 da suka rasa rayukansu.

A yankin kudancin kasar kuwa, shiyar kudu maso Yammacin Najeriya na da mutane 194 da suka rasa rayukansu, sai shiyar Kudu maso Kudu da ke biye masa da mutane 161, yayin da shiyar Kudu mao Gabas ke da mutane 158.

A bangaren garkuwa da mutane, daga cikin alkaluman da kamfanin na Beacon ya fitar, da ya nuna cewar anyi garkuwa da mutane dubu daya da 297 daga shiyar Arewa masu Yammacin Najeriya, mutane 421 a shiyar Arewa maso Gabas da 330 a shiyar Arewa ta Tsakiya, da mutum 30 a shiyar Kusu maso Yammaci, 66 a shiyar Kudu maso Kudanci, sai kuma mutum 20 a shiyar Kudu maso Gabas.

Jihohin da aka fi samun kashe-kashe da garkuwa da mutane

A cewar rahoton, jihar Borno ce kan gaba wajen asarar rayuka, inda mutane 517 suka mutu, sai jihar Benue da ke biye mata da mutane 313, an kashe mutane 252 jihar Katsina, a Zamfara kuwa aka kashe mutane 212 sai kuma Kaduna da ke da mutane 206.

A bangaren garkuwa da mutane, jihar Kaduna ce matsalar ta fi kamari a zangon farko na wannan shekarar, inda aka samu mutane 546, sai Zamfara mai mutane 447, a Borno anyi garkuwa da mutane 340, a Katsina 252 sai babban birnin kasar Abuja da aka yi garkuwa da mutane 102.

Wannan rahoto na kamfanin tsaro na Beacon Security and Intelligence Limited, ya ci karo da batun da mai baiwa shugaban kasar shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu yayi, na cewar an samu raguwar matsalar.

Haka nan a farkon watannan ne ministan tsaron Najeriya Muhammad Badaru Abubakar, ya bayyana cewar an samu gagaruwar nasara wajen yaki da ta’addanci a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.