Isa ga babban shafi
Najeriya

An kakkabe Boko Haram a Adamawa

Rundunar Sojin Najeriya ta yi ikirarin cewa dakarunta sun kakkabe mayakan Boko Haram gaba daya a Jihar Adamawa da ke cikin jihohi uku da aka kafa dokar ta-baci. Cikin wata sanarwa da rundunar Sojin ta fitar a Twitter, ta ce dakarun kasar sun yi nasarar kakkabe mayakan Boko Haram a Madagali.

Taswirar Adamawa a Najeriya
Taswirar Adamawa a Najeriya www.medianews.net
Talla

Sanarwar ta ce Madagali ne gari na karshe da aka kwato daga hannun Boko Haram a Jihar Adamawa, kuma an kwato garin ne ba tare da wani Sojan kasar ya samu rauni ba.

Mayakan Boko Haram sun karbe ikon garin Madagali ne a watan Nuwamban bara.

A makon jiya, shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kwarmata cewa dakarun kasar za su kakkabe mayakan Boko Haram a Jihohin Adamawa da Yobe cikin ‘yan kwanaki kafin su ‘yantar da Borno tsakanin makwanni uku masu zuwa.

Tun a watan Mayun 2013 aka kafa wa Jihohin uku na arewacin Najeriya dokar ta-baci, amma cikin dokar ne mayakan Boko Haram suka kwace ikon garuruwa da dama a yankin.

Dakarun Najeriya dai na samun taimako ne daga dakarun kasashen Chadi da Nijar da Kamaru da ke bakwabta da kasar.

Kuma yanzu Gwamnatin Najeriya ta ce kimanin garuruwa 36 aka kwato tun lokacin dakarun makwabtan kasashe suka kaddamar da yaki da Boko Haram.

Barazanar Boko Haram ne dai ya sa hukumar zabe ta dage lokacin gudanar da babban zabe a Najeriya saboda gargadin da hukumomin tsaro suka yi na rashin garantin tsaro a zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.