Isa ga babban shafi
Najeriya

An kwato garuruwa 36 daga hannun Boko Haram

Hukumomin tsaro a Najeriya sun an yi nasarar kwato garuruwa 36 daga lokacin da dakarun kasar da na makwabta suka kaddamar da farmaki akan mayakan Boko Haram da suka kwace ikon garuruwan a Jahohin Borno da Yobe da Adamawa da ke arewa maso gabacin kasar.

Dakarun Chadi da ke fada Boko Haram a Najeriya
Dakarun Chadi da ke fada Boko Haram a Najeriya REUTERS/Emmanuel Braun
Talla

Mai magana da yawun hukumomin tsaron Najeriya Mike Omeri, ya ce kwato garuruwan wata alama ce da ke tabbatar da cewa ana dab da murkushe kungiyar Boko Haram.

Sannan ya jinjina wa kasashe uku Chadi da Kamaru da Jamhuriyar Nijar da ke taimaka wa Najeriya fada da Boko Haram.

Tun dai lokacin da makwabtan Najeriya suka kaddamar da yaki da Boko Haram, hukumomin kasar ke ikirarin jagorantar yakin, amma masana da mutanen yankin da rikicin ya shafa na cewa dakarun Chadi ne ke samun gagarumar nasara akan Boko Haram.

Matsalar Boko Haram ne dai ya sa aka dage lokacin zaben Najeriya daga ranar 14 ga watan Fabrairu zuwa 28 ga watan Maris. Wasu ‘yan kasar na ganin matakin dage zaben na da nasaba da siyasa domin ba Shugaba Goodluck Jonathan damar sauya ra’ayin masu jefa kuri’a saboda barazanar da Jam’iyyarsa ke fuskanta daga ‘Yan adawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.