Isa ga babban shafi
Nijar

Dakarun Nijar sun kashe ‘Yan Boko Haram sama da 500

Gwamnatin Nijar tace dakarunta sun kashe ‘Yan Boko Haram sama da 500 tun lokacin da suka kaddamar da yaki akan mayakan na Najeriya da ke yin barazana a kasar. Gwamnatin ta fadi adadin ne yayin da ta ke bayyana sakamakon ayyukan Sojojin kasar da ke fada da Boko Haram a yankin Diffa.

Motocin Boko Haram da dakarun Nijar da Chadi suka kwace
Motocin Boko Haram da dakarun Nijar da Chadi suka kwace RFI/Madjiasra Nako
Talla

Gwamnatin Nijar ta shaidawa manema labarai dalla-dalla game da abin da ya shafi ayyukan Sojojin kasar da ke fada da Boko Haram.

Kakakin rundunar ‘Yan sandan Nijar Kaftin Adili Toro ya ce an kashe sojawa 24 tare da jikkata 38 tun lokacin da suka kaddamar da yaki da Boko Haram.

Adili ya ce dakarun Nijar sun kashe ‘Yan Boko Haram 513, kuma 212 an kashe su ne a yankin Bosso na Diffa.

Dakarun Nijar dai sun kaddamar da yaki ne akan Boko Haram bayan mayakan sun tsallako yankin Diffa da ke makwabtaka da Najeriya.

A cikin makon nan dakarun Nijar da Chadi sun yi nasarar kwato garin Damasak da Boko Haram ta kwace a watan Nuwamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.