Isa ga babban shafi
Boko Haram

Mayakan IS sun yi na’am da tayin Boko Haram

Kungiyar Mayakan IS da ke da’awar Jihadi a kasashen Iraqi da Syria sun amince da tayin da mayakan Boko Haram na Najeriya suka yi na nuna goyon baya tare da neman tafiyar da ayyukansu tare, kamar yadda IS ta aiko da sakon sauti wani yana amincewa da tayin na Boko Haram a madadinta.

Shugaban Mayakan IS Abu Bakr al-Baghdadi.
Shugaban Mayakan IS Abu Bakr al-Baghdadi. REUTERS/Social Media Website via Reuters TV
Talla

Wani sakon murya da aka fitar a yammacin Alhamis ya bayyana wani da ke cewa shi ne Kakakin kungiyar IS mai suna Mohammed al-Adnani, yana amincewa da tayin da kungiyar Boko Haram ta yi.

A cikin sakon na tsawon minti 30, Adnani ya yi watsi da ikirarin dakarun Iraqi da na Amurka na samun galaba akansu tare da yin kira ga musulmin yammacin Afrika su ba Mayakan Boko Haram goyon baya.

Mayakan IS dai sun karbe yankuna da dama a Iraqi da Syria tare da ayyana kafa sabuwar daula.

Yanzu Mayakan Boko Haram na Najeriya na cikin kungiyoyi masu da’awar jihadi a Masar da Libya da Pakistan da suka yi mubaya’a ga Mayakan IS.

A ranar Assabar ne shugaban Boko Haram Abubakarar Shekau ya bayyana yin mubaya’a ga shugaban Mayakan IS Abu Bakr al Baghdadi.

Tashe tashen hankulan da ke da alaka da kungiyar Boko Haram sun yi sanadiyyar rasa ran akalla mutane dubu goma sha uku, yayin da wasu miliyan guda da rabi suka tsere daga gidajensu.

Barazanar Boko Haram yanzu kuma ta shafi kasashen Kamaru da Chadi da Nijar da ke makwabtaka da Najeriya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.