Isa ga babban shafi
Tennis

Serena za ta kafa tarihi idan ta lashe US Open a bana

A yau Litinin ne ake soma gasar US Open daya daga cikin manyan gasannin Tennis a duniya. Kuma a ranar farko manyan zaratan Tennis din na duniya Novak Djokovic da Rafeal nadal da Serena Williams za su fara kece raini.

Serena Williams Jarumar Tennis ta duniya
Serena Williams Jarumar Tennis ta duniya USA Today Sports/Dan Hamilton
Talla

Ido zai koma ga Serena wacce ake ganin za ta lashe kofin na US Open a bangaren mata bayan ta lashe sauran manyan gasannin Tennis din na duniya da suka hada da Austrlian Open da French Open da Wimbledon a bana.

Idan dai Senera ta lashe US Open za ta kasance ‘yar wasan Tennis ta farko da ta lashe manyan kofunan Tennis tun Steffi Graf da ta lashe manyan kofunan a 1998.

A yau Serena za ta fara kece raini ne tsakaninta da ‘Yar wasan Rasha Vitalia Diatchenko.

Jarumar Tennis din Rasha Maria sharapova ta fice gasar ta US Open saboda raunin da ta ke fama da shi a kafar dama, matakin da zai rage wa Serena barazana a gasar .

Djokovic kuma na harin lashe manyan kofunan Tennis guda uku a bana bayan ya lashe Wimbledon da Australian Open.

Wawrinka ne ya haramtawa Djokovic lashe a gasar Roland Garros ta Faransa a bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.