Isa ga babban shafi
CAF

CAF za ta dauki mataki akan mutuwar Ebosse a fili

Shugaban hukumar kwallon Afrika Issa Hayatou ya yi Allah waddai da jifar Dan wasan Kamaru Albert Ebosse da aka yi a cikin fili a kasar Algeria wanda ya yi sanadin mutuwarsa. Wani daga cikin ‘Yan kallo ne ya jefi dan wasan, kuma ya mutu ne bayan an garzaya da shi zuwa Asibiti.

Dan kasar Kamaru Albert Ebossé, da aka jefa a fili kuma ya yi sanadin mutuwarsa a Algeria
Dan kasar Kamaru Albert Ebossé, da aka jefa a fili kuma ya yi sanadin mutuwarsa a Algeria DR/Facebook
Talla

Dan wasan na Kamaru shi ne ya fara jefawa kungiyar shi JS Kabylie kwallo a raga amma abokiyar hamayya USM Alger ita ce ta lashe wasan ci 2-1.

Shugaban Hukumar kwallon Afirka Issa Hayatou yace ba zasu amince aika-aika ba daga yan tayar da tsaune tsaye, don haka dole su dauki mataki akai

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.