Isa ga babban shafi
La liga

Granada ta doke Barca, Atletico da lallasa Getafe

Barcelona ta sake nutsewa a teburin gasar La liga a Spain bayan ta sha kashi ci 1 da 0 a gidan Granada. Atletico ce ke ci gaba da jagorancin teburin gasar wacce ta lallasa Getafe ci 2-0 a jiya Lahadi, sai dai kuma dan wasanta Diego Costa bai sha da dadi ba domin da makara aka fitar da shi a fili saboda raunin da ya samu.

Lionel Messi tare da 'Yan wasan Barcelona suna juyayi
Lionel Messi tare da 'Yan wasan Barcelona suna juyayi REUTERS/Marcelo del Pozo
Talla

Real Madrid da ke matsayi na biyu a yanzu ta caccasa Almeria ne ci 4 da 0, kuma duk da tazarar maki uku da ke tsakaninta da Atletico, Barcelona na iya taimakawa Real Madrid lashe kofin La liga idan har ta doke Atletico Madrid a fafatawan karshe.

Atletico tana harin lashe kofin La liga ne a karon farko, tsawon shekaru 18.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.