Isa ga babban shafi
FIFA

FIFA ta haramtawa Barcelona sayen ‘Yan wasa

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta haramtawa kungiyar Barcelona ta Spain sayen ‘yan wasa na tsawon kasuwar cinikin ‘yan wasa guda biyu, FIFA kuma ta dauki wannan matakin ne saboda Barcelona ta keta dokokin sayen ‘Yan wasa masu kananan shekaru.

Dan wasan Barcelona, Lionel Messi
Dan wasan Barcelona, Lionel Messi REUTERS/Albert Gea
Talla

Haramcin sayen ‘yan wasan ya shafi tsawon watanni 14, kuma FIFA ta ci tarar Barcelona kudi euro dubu dari uku da sittin da tara.

Yanzu haka FIFA ta ba Barcelona nan da wata uku ta gyra al’marin da ya shafi matasan ‘yan wasa 10.

Amma Zuwa yanzu babu wani martani daga Barcelona, kodayake ana sa ran kungiyar zata fitar da sanarwa akan batun, domin tana da damar ta kalubalantar hukuncin.

Sai dai kuma Barcelona tana da damar shigar da kokenta nan da kwanaki uku a gaban kotun sauraren kararrin wasanni.

Wannan dai wata sabuwar baraka ce da ta kunno kai a Barcelona bayan badakalar cininkin sayen Naymar na Brazil.

Haramcin kuma zai shafi ‘yan wasan Barcelona da ke shirin ficewa kungiyar, musamman Carles Puyol da mai tsaron gidan kungiyar Victor Valdes da yarjejeniyarsu zata kawo karshe a watan Yuni.

A bara ma hukumar FIFA ta taba dakatar da wasu matasan ‘yan wasan Barcelona guda shida daga shiga Gasa saboda irin wannan badakalar.

A tsarin dokar FIFA sai dan wasa ya kai shekara 18 kafin a yi cinikinsa tsakanin wata kungiya zuwa wata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.