Isa ga babban shafi
Zakarun Turai

Man U ta rike Bayern, haka Atletico ta rike Barca

A gasar neman kofin zakarun Nahiyar Turai zagayen gab da kusa da na karshe wato Quarter Finals ko kuma Quart de Final, a daren jiya Man United ta yi kunnen doko da Bayern Munich ci daya kowanne, yayin da ita ma Barcelona ta yi kunnen doki da Atletico Madrid ci daya kowanne.

Karawar Man U Bayern Munich
Karawar Man U Bayern Munich REUTERS/Stefan Wermuth
Talla

An dai fafata ne tsakanin Man United da kuma Bayern Munich a Old Trafford wato a gidan Man U.

Man United ce ta soma zura kwallo a ragar Bayern Munich ana minti na 58 da soma karawar, kuma Vidic ne ya zura wannan kwallo. To sai dai dan wasan Bayern Schweinsteiger ya rama wannan ci lokacin da aka shiga minti na 66 da soma wasan. Dag bisani an fitar da Schweinsteiger daga filin wasa bayan da alkali Carlos Velasco Carballo ya ba shi jan kati bayan ya yi karo da Rooney.

Mai horas da ‘yan wasa na Man United David Moyes, ya ce ya gamsu matuka dangane da rawar da da ‘yan wasansa suka taka a daren na jiya.

 

 

 

 

Wasa na biyu da aka buga cikin daren jiya a gasar ta neman kofin Zakarun Nahiyar Turai zagayen da ke biye wa na kusa da na karshe, Barcelona ce ta karbi bakuncin Atletico Madrid a filin wasa na Nou Camp.

To shi ma dai wannan wasa kamar wanda aka buga a Old Trafford an tahsi ne ci daya a tsakanin wadannan kulob biyu. Diago Coasta na Atletico Madirid ne ya soma zura kwallo a ragar Barcelona ana mintuna na 56 da soma wasa, to sai dai Neymar na Barcelona ya rama wannan ci a daidai lokacin da aka shiga mintuna 71 da soma karawar.

Dukkanin bangarorin biyu dai su yi iya kokarinsu domin sauye wannan sakamako amma ba tare da sun samu nasara ba har aka tashi ana ci daya kowanne.

A ranar laraba ta makon gobe ne dai wato 9 ga wannan wata na afrilu ne za a je zagaye na biyu inda Barcelona za ta yi tattaki zuwa Madrid, yayin da ita kuwa Bayern Munich za ta karbi bakuncin Man United.

PSG za ta karbi Chelsea a marecen yau

To a marecen yau kuwa PSG ta Faransa ce za ta karbi bakuncin Chelsea ta Ingila, yayin Real Madrid ta Spain ke shirin karbar Borussia Dortmund ta Jamus duk a gasar ta neman kofin zakarun nahiyar Turai a matakin Quarter Finals.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.