Isa ga babban shafi
Ingila

Sunderland ta doke Manchester United

Manchester United ta sake shan kashi a hannun Sunderland ci 2-1 a gasar gida ta Capital One karawar farko, bayan Tottenham Hotspur da Swansea City sun ba United kashi a makwannin da suka gabata.

Ryan Giggs na Manchester United ya dafe kai a wasansu da Sunderland da ya ci kansu.
Ryan Giggs na Manchester United ya dafe kai a wasansu da Sunderland da ya ci kansu. REUTERS/Nigel Roddis
Talla

A wannan karon ma David Moyes kocin Manchester ya soki alkalin wasa akan bugun daga kai sai mai tsaron gida da ya ba Sunderland bayan an dawo hutun rabin lokaci wanda ya ba Fabio Borini damar zira kwallo ta biyu a ragar Manchester.

Manchester dai a bana na fuskantar yanayi a karkashin David Moyes wanda ya gaji Ferguson domin Yanzu haka teburin Premier ya yi wa United nisa domin tazarar maki 11 ne tsakaninta da Arsenal da ke saman teburin. Kuma an yi waje da ita a gasar FA.

Ryan Giggs ne na Manchester a jiya Talata ya fara cin kansu kafin daga bisani Vidic ya barke kwallon. Amma a kwallo ta biyu Moyes yace an ha’incesu.

A yau laraba ne Manchester City zata karbi bakuncin West Ham a karawa ta farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.