Isa ga babban shafi
Premier League

Moyes ya amsa samun baraka a United

David Moyes yace abubuwa fa sun masa tsauri a Manchester United, yana mai amsa cewa be shiga da kafar dama ba a Old Trafford saboda kashin da ake ba shi a Premier League.

Kocin Manchester United David Moyes
Kocin Manchester United David Moyes REUTERS/Stefan Wermuth
Talla

Manchester United da ke rike da kofin Premier, amma yanzu tana matsayi na 9 ne a teburin gasar bayan buga wasanni 15, kuma tazarar maki 13 ne tsakaninta da Arsenal da ke jagorancin teburin gasar.

A baya bayan nan Moyes ya sha kashi a hannun Everton da Newscastle cikin kwanaki 4, kuma a gobe Talata ne zai kara da Shakhtar Donetsk a gasar zakarun Turai.

Sai dai kuma Moyes yace akwai matakai da ya ke dauka domin magance barakar da ya samu tun a tashin farko bayan ya gaji Sir Alex Ferguson.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.