Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Littafin rayuwar Ferguson ya shiga kasuwa

A yau Alhamis ne za’a fara sayar da litattafin rayuwar Tsohon Kocin Manchester Sir Alex Ferguson wanda ya yi ritaya bayan ya kwashe shekaru sama da 20 a Old Trafford yana aikin horar da ‘Yan wasa.

Sir Alex Ferguson Tsohon Kocin Manchester yana rike da littafin rayuwar shi
Sir Alex Ferguson Tsohon Kocin Manchester yana rike da littafin rayuwar shi REUTERS/Luke MacGregor
Talla

A cikin litattafin na Ferguson wanda aka kaddamar a ranar Talata, Tsohon kocin ya kwarmata huldarsa da dangantakarsa da ‘Yan wasan da ya horar.

Amma akwai suka yanzu da kalaman na Ferguson a cikin litattafin suka janyo daga ‘yan wasan shi.

Wayne Rooney na Manchester yace be damu da ikirarin Ferguson ba inda a cikin litatttafin tsohon kocin na Manchester yace ya shiga damuwa game da makomar Rooney dab da zai yi ritaya tare da ikirarin cewa Rooney da kansa ne ya nemi ya fice United a watan Mayu.

Sai dai kuma a wata hira da aka yi da Ferguson bayan kaddamar da litaffin, Tsohon kocin yace Rooney be gabatar da bukatar ficewa ba.

Amma bayan kammala wasan Manchester a daren Alhamis a gasar Zakarun Turai, Rooney ya shaidawa Sky Sport cewa tun lokacin da Ferguson ya yi ritaya be yi tozali da shi ba, kuma kalaman Ferguson sun yi karo da juna game da batun ficewar shi Manchester.

A cewar Rooney yanzu ba wannan ne damuwar shi ba domin yana jin dadi karkashin jagorancin sabon kocinsu David Moyes.

A cikin litattafin Ferguson yace ya sayar wa Real Madrid da Beckham ne bayan ya bankade wani dan wasa saboda gardama a lokacin da suka sha kashi a hannun Arsenal a 2003 a gasar FA .

Ferguson yace Beckham ya fara fita ransa ne a lokacin ya ke son nuna wa duniya kansa bayan ya auri mawakiya Victoria Adams a shekarar 2009.

A cikin litattafin kuma Ferguson yace Manchester ta nemi Roy Keane ya fice kungiyar ne bayan ya caccaki abokan wasan shi a wata hira da aka yi da shi a wata kafar Telebijin.

10:26

Ferguson ya yi bankwana da Old Trafford

Amma Ferguson ya bayyana Cristiano Ronaldo wanda ya bar Manchester zuwa Real Madrid a 2009 a matsayin dan wasa mai ilimin kwallo daga cikin ‘Yan wasan da ya horar.

Ferguson mai shekaru 71 ya yi ritaya ne a kakar da ta gabata bayan ya kwashe shekaru 26 yana aikin horar da Manchester United inda ya lashe kofuna 13 na Premier League da kofin zakarun Turai guda biyu da kofin FA guda 5 da kuma Kofin Carling guda 4.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.