Isa ga babban shafi
Premier League

An zabi Ferguson a matsayin gwarzon kocin shekara na gasar Premier

Alex Ferguson wanda ya yi bankwana da Manchester United ya lashe kyautar gwarzon kocin shekara a gasar Premier League ta Ingila, bayan taimakawa United lashe kofin gasar karo na 20.

Mai horar da 'Yan wasan Manchester United, Alex Ferguson
Mai horar da 'Yan wasan Manchester United, Alex Ferguson REUTERS/Phil Noble
Talla

Ferguson ya bayyana yin ritayarsa ne a makon da ya gabata bayan ya kwashe shekaru 26 yana jagorantar kungiyar Manchester United.

Ya kuma lashe kofuna da dama da suka hada da na gasar Premier League da na FA Cup da kuma gasar Zakarun Turai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.