Isa ga babban shafi
Premier League

Tottenham ta doke Manchester United

Kungiyar Tottenham ta bi Manchester United har gida Old Trafford ta doke ta ci 2-1 a gasar Premier ta Ingila da aka gudanar a sabuwar shekara. Hakan ne ya kara nutse Manchester da tazarar maki 11 tsakaninta da kungiyoyin da ke jagorancin teburin gasar a bana.

Mai Horar da 'Yan wasan Manchester United yana korafi ga alkalin wasa bayan an haramta masu Fanalti a wasan da ya sha kashi a hannun Tottenham a Old Trafford a sabuwar shekara.
Mai Horar da 'Yan wasan Manchester United yana korafi ga alkalin wasa bayan an haramta masu Fanalti a wasan da ya sha kashi a hannun Tottenham a Old Trafford a sabuwar shekara. REUTERS/Nigel Roddis
Talla

David Moyes wanda ya sha kashi sau shida a bana ya soki wanda ya yi alkalancin wasan Howard Webb akan be yi wa Manchester adalci ba saboda ya haramta masu fanalti a lokacin da mai tsaron gidan Tottenham ya yi karo da Ashley Young.

Moyes ya bukaci hukumar da ke kula da alkalan wasa ta diba al’amarin domin biya wa United hakkinta.

Kungiyar Arsenal kuma ta doke Cardiff City ne ci 2-0 wanda hakan ya ba Arsenal damar ci gaba da jagorancin teburin Premier. Manchester City da ke bi wa Arsenal ta doke Swansea City ne ci 3-2.

Tazarar maki daya ne kacal tsakanin Arsenal da City sai Chelsea da ke bi masu wacce ta lallasa Southampton ci 3-0.

Liverpool ta huce ne akan Hull City ci 2-0 bayan ta sha kashi a hannun Manchester City da Chelsea, wannan nasarar ce kuma ta ba Liverpool damar haurowa zuwa matsayi na hudu.

Arsene Wenger dai yace ya yi imanin a bana suna kan hanyar lashe kofin Premier bayan shafe shekaru 10 suna yunwar kofin. Sai dai wannan kamar cika baki ne domin babu wata tazara mai girma tsakanin Arsenal da City da kuma Chelsea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.