Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Moyes yana nazarin yin cefanen ‘Yan wasa

David Moyes yace akwai gazawa tare da ‘yan wasan shi don haka yana nazarin shiga kasuwar ‘Yan wasa da aka bude a watan Janairu domin sayen sabbin ‘yan wasa. Wannan kuma na zuwa ne bayan Manchester United ta fice gasar FA bayan ta sha kashi a hannun Swansea City ci 2-1.

David Moyes, na Manchester United
David Moyes, na Manchester United AFP PHOTO/IAN KINGTON
Talla

A bana sau hude ke nan a wasanni shida, Manchester United na shan kashi a gida Old Trafford, kuma wannan ne karo na biyu da Kungiyar ta fice gasar FA tun a zagaye na uku a tsawon shekaru 29.

Manchester United dai ta shiga rudani ne tun zuwan David Moyes daga Everton wanda ya gaji Sir Alex Ferguson bayan ya yi ritaya.

Tun zuwan Moyes dan wasa guda ne tilo Marouane Fellaini, ya sayo daga Everton kuma yanzu yana fuskantar matsin lamba akan ya saye sabbin ‘Yan wasa.

Amma Sabon kocin na Manchester yace yana nazari amma akwai wahala ya shiga kasuwar a watan Janairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.