Isa ga babban shafi
Wasanni

Wani magoyin bayan Manchester United ya nemi a kawo wa kungiyar dauki

‘Yan sandan kasar Britaniya sun ce wani mutum magoyin bayan kungiyar Manchester United, da ya sha giya ya yi tatil, ya kira lambar nan ta 999, da ake kira don neman agajin gaggawa a kasar. Mutumin ya kira lambar ne don neman ya yi magana da tsohon manajan kungiyar ta United Sir Alex Ferguson.‘Yan sandan sun ce mutumin ya kira su ne, bayan da ranar Laraba kungiyar Sunderland ta bi United har gida, ta lallasa su a bugun daga kai sai mai tsaron gida, a wasan kusa da na karshe, na gasar League Cup da aka yi a Old Trafford.Dama dai United sun fice daga gasar FA Cup, kuma a gasar Primiyan kasar Ingila sai sauka daga Tebur suke yi, inda Arsenal da ke samar tebur ta basu tazarar maki 14, tun lokacin da manaja David Moyes ya karbi ragamar Kulob din. 

Manajan kungiyar Manchester United  David Moyes
Manajan kungiyar Manchester United David Moyes
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.