Isa ga babban shafi
Wasanni

Chelsea ta doke Man United ci 3-1 a gasar Premier ta Ingila

A gasar Premier ta kasar Ingila a jiya an fafata tsakanin Chelsea da kuma Man United, inda aka tashi wasan Chelsea na da nasara wato ci 3 da 1.

Samuel Eto'o na Chelsea a karawarsu da Manchester United.
Samuel Eto'o na Chelsea a karawarsu da Manchester United. REUTERS/Stefan Wermuth
Talla

A gasar Premier ta kasar Ingila a jiya an fafata tsakanin Chelsea da kuma Man United, inda aka tashi wasan Chelsea na da nasara wato ci 3 da 1.

Tun kafin a je hutun rabin lokaci ne dai Samuel Eto ya samu nasarar zura kwallaye 2 a ragar Man United, yayin da kuma aka dawo daga hutun rabin lokaci na farko ya sake zuwa wata kwallon anan mintuna na 49.

An ci gaba da fafatawa tsakanin club din biyu har zuwa minti na 78, inda Hermandez ya samu nasarar saka kwallo a ragar Chelsea, lamarin da ya sa aka tashi wasan ci 3 da 1. To sai dai kuma Man United ta yi wannan karawa ne ba tare da ‘yan wasanta biyu ba wato Rooney da kuma Van Persie.

To kafin a buga wannan wasa tsakanin Chelsea da kuma Man Utd a jiya da rana an kara tsakanin Tottenham da kuma Swansea, inda aka tashi wasan I 1 da 3 wato Tottenham na da nasara.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.