Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

La liga: Karawar Clasico ta ja hankali

Jaridun Spain a yau Litinin sun ce karawar da aka yi a jiya Lahadi tsakanin Real Madrid da Barcelona ita ce fafatawar da ba’a taba gani ba a tarihin karawar kungiyoyin biyu masu hammaya da juna a duniyar kwallon Turai.

Dan wasan Barcelona Lionel Messi a kusa da Cristiano Ronaldo na Real Madrid a karawar Clasico.
Dan wasan Barcelona Lionel Messi a kusa da Cristiano Ronaldo na Real Madrid a karawar Clasico. Eurosport
Talla

An yi ruwan kwallaye ne guda bakwai inda Barcelona ta lashe wasan da ci 4 da 3 akan Real Madrid.

Batun Messi ne ya mamaye jaridun Spain musamman a yankin Cataloniya wanda ya zira kwallaye uku a karawar, kuma a jiya ne ya kafa tarihi a matsayin wanda ya fi yawan zira kwallaye a tarihin Classico.

Jaridar Daily Marca, tace Barcelona ta samu nasara a daren da aka yi karawar kwallo da ruwan kwallaye. Jaridar tace ba za’a taba mantawa da karawar Lahadi ba a tarhin kungiyoyin biyu da Jaridar tace za su ci gaba da adawa har abada.

Jaridar Marca ta maka babban labarinta mai taken “Yanzu aka fara League”, domin yanzu tazarar maki daya ne Real Madrid da Atlecito Madrid suka ba Barcelona da ke matsayi na uku.

Sai dai kuma a nata bangaren, Jaridar Daily AS da ke adawa da Marca, ta buga labari ne mai taken “fanalti uku, kwallaye bakwai da jan kati guda”, tana mai sharhi akan yadda Barcelona ta samu sa’ar Real Madrid a Santiago.

Akwai sukar alkalin wasa da Cristiano Ronaldo na Real Madrid ya yi, akan Alberto Undiano Mallenco wanda ya yi alkalancin wasan Clasico a daren Lahadi.

Ronaldo ne alkalin wasan ya fara ba Fanalti a ragar Barcelona amma kuma Dan wasan yace alkalancin akwai surkulle a ciki, musamman jan kati karo na 19 da aka sallami Ramos a filin wasan.

Za’a dai sake karawa tsakanin Barcelona da Real Madrid a gasar Copa del Ray ko gasar Sarki a Spain, wata kila kuma kungiyoyin zasu iya sake haduwa a gasar zakarun Turai idan har sun tsallake a zagaye na gaba a gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.