Isa ga babban shafi
Champions League

An hada Manchester da Bayern Munich

Manchester United zata fara karbar bakuncin Bayern Munich a Old Trafford a gasar Zakarun Turai zagayen Kwata Fainal. An hada kuma Barcelona da Atletico Madrid ‘yan gida guda. Real Madrid zata sake haduwa da Borussia Dortmund. Chelsea zata kara ne da Paris Saint-Germain.

Manyan 'Yan wasa daga kungiyoyin da aka hada kungiyoyinsu a zagayen kwata fainal a gasar zakarun Turai
Manyan 'Yan wasa daga kungiyoyin da aka hada kungiyoyinsu a zagayen kwata fainal a gasar zakarun Turai FIFAtwitter
Talla

Tarihi ne za’a maimaita tsakanin Bayern Munich da Manchester United a wasan karshe da kungiyoyin biyu suka fafata a shekarar 1999 a Barcelona.

Barcelona zata fara karbar bakuncin abokiyar adawarta a La liga Atletico Madrid a filin wasa na Nou Camp.

Kungiyar Chelsea zata fara kai wa Paris Saint-Germain ne ziyara a Paris.

Real Madrid da ke harin lashe kofin karo na 10 zata sake haduwa ne da Borussia Dortmund, da ta doke ta a bara zagayen dab da na karshe.

Za’a fara karawa ta farko ne a ranar 1 ga watan Afrilu a wasannin zagayen Kwata Fainal, sannan a yi karawa ta biyu ne a ranakun 8 da 9 na watan Afrilu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.