Isa ga babban shafi
Champions League

Van Persie ya kubutar da Manchester

Robin van Persie ya ceto Manchester United a gasar zakarun Turai wanda ya taimakawa kungiyar tsallakewa zuwa zagayen kwata Fainal bayan ya yi ruwan kwallaye uku a ragar Olympiakos, inda aka tashi wasan ci 3-0 a filin wasan na Old Trafford.

Robin Van Persie ya rungume Wayne Rooney a karawarsu da Olympiakos
Robin Van Persie ya rungume Wayne Rooney a karawarsu da Olympiakos REUTERS/Phil Noble
Talla

Manchester ta rama dukan da Olympiakos, ci 2 da 0 a karawa ta farko a kasar Girka. Wannan ne karon farko da United ta rama ratar kwallaye biyu a gasar zakarun Turai, kuma yanzu kungiya ta shida a jerin kungiyoyiyn Turai a tarihin gasar.

Tuni dai David Moyes da ya sha kashi a hannun Liverpool a karshen mako a Premier ya bayyana farin cikinsa da nasarar da suka samu a daren jiya Laraba, wanda hakan kuma zai dan sassauta kalubalen da Kocin ke fuskata bayan ya gaji Sir Alex Ferguson.

A daya bangaren kuma Borussia Dortmund ta tsallake zuwa kwata Fainal duk da ta sha kashi ci 2-1 a gidan Zenit St Petersburg a daren jiya.

Kwallayen da Dortmund ta zira guda 4 a karawa ta farko su ne suka taimaka wa kungiyar ta Jamus samun nasarar haurawa Kwata fainal da jimillar kwallaye ci 5-4.

Yanzu United da Dortmund sun cike gurbin kungiyoyi 8 da za su kara a Kwata Fainal bayan tuni Bayern Munich da Barcelona da Real Madrid da Atletico Madrid da Paris Saint-Germain da suka tsallake, inda a gobe Juma’a ne za’a hada kungiyoyin da zasu kara a watan Afrilu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.