Isa ga babban shafi
Champions League

Chelsea da Madrid sun yi waje da Gala da Schalke

Chelsea da Real Madrid sun tsallake zuwa zagayen kwata Fainal a gasar zakarun Turai bayan Chelsea ta samu nasara akan Galatasaray a Stanford Bridge da jimillar kwallaye ci 3-1. Real Madrid kuma ta sake lallasa Schalke 3-1 a karawar da suka yi Santiago Bernabeu, wannan ya ba Madrid nasarar tsallakewa da jimillar kwallaye ci 9-2.

Samuel Eto'o na Chelsea a karawarsu da Manchester United.
Samuel Eto'o na Chelsea a karawarsu da Manchester United. REUTERS/Stefan Wermuth
Talla

Samuel Eto’o da Gary Cahill ne suka zirawa Chelsea kwallayenta a raga a yayin da kuma Cristiano Ronaldo ya jefa wa Real Madrid kwallaye biyu a ragar Schalke 04.

Hakan ke nuna Kungiyar Chelsea ita ce yanzu kungiya tilo daga Ingila da ta tsallake a gasar zakarun Turai bayan an yi waje da Manchester City da Arsenal.

Yanzu Real Madrid da Chelsea sun bi sahun Bayern mai rike kofin gasar da Atletico Madrid da Barcelona da Paris Saint-Germain wadanda tuni suka tsallake zuwa kwata fainal inda a ranar Jum’a za’a hada kungiyoyin da zasu kara a zagayen.

Bayan kammala wasan Chelsea, Jose Mourinho na ya bugi kirji yana cewa baya jin tsoron haduwa da manyan kungiyoyin Turai a zagaye na gaba, irin Bayern Munich da Real Madrid da Barcelona.

A yau Laraba, a filin wasa na Old Trafford, Manchester United zata yi kokarin rama duka da Olympiakos ta yi mata ci 2-0 a karawa ta farko idan har United zata iya tsallakewa a zagaye na gaba.

Akwai wasa tsakanin Borussia Dortmund da Zenit St Petersburg, inda Dortmund zata nemi kare nasarar da ta samu a karawa ta farko ci 4-2.

Kafin wasan Kungiyar Zenit ta ayyana sunan Andre Villas-Boas tsohon kocin Chelsea da Tottenham a matsayin sabon mai horar da ‘Yan wasanta inda a gobe Alhamis Kungiyar tace zai sa hannu akan kwataragin da suka kalla domin maye gurbin kocin da kungiyar ta sallama Luciano Spalletti.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.