Chelsea ta nemi a kare rayukan magoya bayanta a Turkiya
Kungiyar Galatasaray zata karbi bakuncin Chelsea a birnin Istanbul inda Dideiar Drgba na Cote d’Ivoire zai hadu da tsoffin abokan wasan shi. Sai dai kuma kungiyar Chelsea ta tabbatar da labarin wani hari da aka kai wa magoya bayanta guda biyu a birnin Istanbul kafin fafatawarta da Galatasaray.
Wallafawa ranar:
Yanzu haka zanga-zanga ce ake ci gaba da gudanarwa a kasar Turkiya, kuma akwai bukatar da kungiyar Chelsea ta gabatar ga Jami’an tsaron kasar domin kare rayukan magoya bayanta a filin wasa.
An dai taba kashe wasu magoya bayan kungiyar Leeds United guda biyu a birnin Istanbul a lokacin da zata kara da Galatasaray a 2000.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu