Isa ga babban shafi
La liga

Sevilla ta doke Madrid

Real Madrid ta sake shan kashi a hannun Sevilla ci 2-1 bayan ba ta ji da dadi ba a hannun Barcelona. Wannan sakamakon wasan ya sa Real Madrid ta dawo matsayi na uku yayin da Atletico Madrid ta dare teburin La liga da tazarar maki 3 tsakaninsu bayan ta doke Granada ci 1-0.

Cristiano ya dafe kai a karawar Real Madrid da Sevilla
Cristiano ya dafe kai a karawar Real Madrid da Sevilla REUTERS/Marcelo del Pozo
Talla

Barcelona ce yanzu a matsayi na biyu, da tazarar maki biyu tsakaninta da Real Madrid.
Dan kasar Colombia Carlos Bacca shi ne ya jefa dukkanin kwallayen biyu a ragar Madrid bayan Cristiano ya zira kwallo ta farko.

Bayan kammala wasan Kocin Real Madrid Carlo Anceloti yace yana da yakinin zasu iya lashe kofin La liga a bana duk da cewa sun sha kashi sau biyu a cikin kwanaki 4.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.