Akwai sauran aiki a gaban Brazil kafin 2014, inji Romario
Romario Tsohon dan wasan Brazil yace basu da tabbaci ko kasar ta shirya 100 bisa 100 wajen daukar nauyin gasar cin kofin duniya da za’a gudanar a shekarar 2014. A lokacn da tsohon dan wasan ke ganawa da manema labarai, yace filayen wasa 12 da kasar ta yi alkawalin za’a buga wasan, ba zasu samu ba sai dai 10 kafin a fara gasar.
Wallafawa ranar:
Romario ya yi gargadin cewa kudaden da suke tunanin za’a kashe domin daukar nauyin gasar sun zarce kiyasin da suka yi wato dala biliyan 44 zuwa dala Biliyan 55.5.
Da farko dai Ministan wasannin kasar ne Aldo Rebelo a bara ya shiadawa duniya cewa kasar zata samar da filayen wasa 12 domin daukar nauyin gasar tare da ikirarin za’a kammala su kafin lokacin gasar.
Sai dai Romario wanda tsohon an wasa ne a kasar kuma wanda ya yi fice a Nahiyar Turai dama duniya yana kalubalantar kwamitin da aka daura wa alhakin shirya daukar nauyin gasar
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu