Isa ga babban shafi
Faransa

'Yan adawa sun yi rinjaye a Majalisar Dattawan Faransa

‘Yan adawa sun karbe ragamar jagorancin Majalisar Dattawan kasar Faransa, kamar dai yadda sakamakon zaben sabunta wani bangare na Majalisar da aka gudanar a jiya lahadi ke nunawa.

Majalisar Dattawan Faransa
Majalisar Dattawan Faransa
Talla

Zaben na jiya wanda aka lokacinsa aka sabunta kashi 1 cikin 3 na wakilan Majalisar Dattawan, sakamakonsa na mai tabbatar da cewa a halin yanzu jam’iyyar UMP ta tsohon shugaban kasar Nicolas Sarkozy da abokannin kawancenta na da kujeru 188 daga cikin 348 da ke cikin cikin zauren majalisar.

Wani abu a game da wannan zabe shi ne yadda jam’iyyar ‘yan kishin kasa ta Front National ta samu karin kujera daya a cikin zauren majalisar, lamarin da ake kallo a matsayin babban koma-baya ga jam’iyyar ‘yan gurguzu ta shugaba Francois Hollande da ke kan karagar mulki.

Wannan dai shi ne karo na biyu a cikin wannan shekara da jam’iyyar shugaba Hollande ke shan kashi a hannun ‘yan adawa, baya ga kashin da ta sha a cikin watan maris da ya gabata lokacin da aka gudanar da zaben kananan hukumomi.

Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a kasar ta Faransa, ta nuna cewa matukar dai aka je zagaye na biyu a zaben shugabancin kasar na shekara ta 2017, to ko shakka babu jagorar jam’iyyar ta masu ra’ayin rikau Marine Le Pen za ta iya doke shugaba Hollande a zaben.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.