Isa ga babban shafi
Amurka-Iraqi

Amurka ta bada Umurnin dirarwa kungiyar ISIS ta Iraqi da Siriya

Shugaban Kasar Amurka Barack Obama ya bada umurnin kai hare-haren sama kan mayakan kungiyar ISIS a cikin kasar Siriya da kuma fadada kai hare-haren zuwa kasar Iraqi

alt-market.com
Talla

A jawabin da ya yiwa Amurka daren jiya, shugaban yayi alkawarin sake gina dakarun Iraqi da kuma taimakawa ‘Yan Tawayen Siriya da makamai, inda yake cewar bukatarsu ita ce murkushe ‘Yan Tawayen kungiyar ta ISIS. wannan kuma ya nuna cewar Amurka ta karbe fadan daga Sojin kasa-da-kasa masu fada da mayakan jihadin.

Obama ya ce “Na fada karara cewar za mu dakusar da ‘yan ta’adda da suka takali kasarmu fada duk inda suke.

Ina nufin ba zan fasa daukar mataki akan kungiyar ISIS ba a kasashen Siriya da Iraqi.

Wannan alhaki ne da ya rataya a kaina a matsayin shugaban kasar Amurka, kuma duk wanda ya yi barazana ga Amurka zai rasa mafaka a Duniya”

Masu lura da al’amurra dai na ganin wannan matakin da Amurka ta dauka a matsayin komal-baya ga ikrarin da ta yi a baya na cewar ba tana son mamaye kasar Iraki ba ne.

Iraki dai ta sha fama da matsalar kai hare-haren da ake dora alhakinsu ga kungiyoyi masu tada kayar baya, sai dai wani abin da ke daukar hankali a nan shi ne yanda amurka za ta yi da ‘ya’yan kungiyar ISIS na Siriya inda itama take da ‘yan tawaye masu fada da gwamnatin Bashar al-Assad shekaru da dama da suka gabata, gashi kuma Iran na taimakawa Bashar al-Assad a kallon Hadarin Kajin da ke faruwa tsakaninshi da kasar ta Amurka.

Iran dai ba za ta bar Amurka mike Kafafuwa a Siriya kamar yanda ta yi a Iraqi ba, musamman lura da yanda Amurka ke bukatar yin gaban kanta a Yaki duk kasar da ta shiga.

Ida nana iya tunawa a baya an ruwaito shugaban kasar Amurkar Barack Obama na fada cewar ba zata hada kai da Siriya domin yaki da ‘yan kungiyar ISIS ba, saboda rashin jituear da ke tsakaninsu da shugaban kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.