Isa ga babban shafi

Yarjejeniyar tsagaita wuta na tangal tangal a Ukraine

Wasu abubuwa da suka fashe a gabashin kasar Ukraine, sun sa fargabar rashin dorewar yarjejeniyar tsagaita wutar da ta fara aiki jiya Asabar. An ji karar fashewar abubuwa, an kuma ga hayaki ya turnuke sama a birnin Mariupol na gabar ruwa, dake hannun dakarun gwamnati a gabashin kasar.Sabon tashin hankalin na zuwa ne ‘yan sa’oi kadan, bayan shugaban kasar ta Ukraine Petro Poroshenko da takwaranshi na Rasha Vladimir Putin sun gana ta wayar tarho, inda suka tabbatar wa juna yarjejeniyar da aka kulla ranar Juma’a tana aiki.Yanzu haka mazauna yankin suna ci gaba da bayyana fargabar barkewar sabon rikici, inda harbin bindiga da makamai masu roka da aka harba, suka yi sanadiyyar rushewar gidaje da dama a yankin.Yanzu dukkan bangarorin 2 sun ci gaba da nuna dan yatsa ga juna, saboda barkewar sabon rikicin. 

Shugaban kasar Ukraine, Petro Porochenko da takwaranshi na Rasha Vladmir Putin
Shugaban kasar Ukraine, Petro Porochenko da takwaranshi na Rasha Vladmir Putin ©Reuters.
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.