Isa ga babban shafi
Rasha-EU-Ukraine

Rasha ta nemi kasashen EU su sake tunani kan shirin kara mata takunkumai

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya nemi kasashen Turai su yi amfani da hankali, su kaucewa sanya wa kasar karin Takunkumai, lamarin da yace iya yin illa ga dukkan bangarorin 2. Kalaman na Mr Putin sune na farko tun bayan da kasashen Turai suka yi barazanar sanya wa Rasha karin takunkumai, sakamakon rawar da ake zargin tana takawa a rikicin kasar Ukraine.Shugaban na Rasha yace yana fata za ayi amfani da hankali, kuma Rasha da sauran kasashen dake takun saka, ba zasu jawo matsala ba, ta hanyar tsikarin juna.Kalaman, na zuwa ne kwana guda bayan shugabannin kasashen EU sun baiwa Rasha mako daya, ko dai ta sauya rawar da take takawa a rikicin kasar ta Ukraine, ko kuwa a kara mata sabbin takunkumai.Ana ci gaba da samun fargabar rikicin zai iya mamaye daukacin nahiyar Turai, bayan da wasu rahotanni suka ce hukumomin birnin Moscow sun tura dakaru, don tallafawa ‘yan tawaye a kudancin Ukraine.Dama jami’an gwamnatin Rasha sun ce suna shirin daukar matakan fansa, kan takunkuman da kasashen yamma zasu sake sanya wa kasar, bayan sun hana shiga da kayan abinci da dama daga kasashen Turai da Amurka. 

shugaban kasar Rasha , Vladimir Putin,
shugaban kasar Rasha , Vladimir Putin,
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.