Isa ga babban shafi
Fransa-Iraki

Faransa ba ta da niyyar aika sojoji zuwa Iraki

Ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius, wanda ke gudanar da ziyarar aiki a kasar Iraki, ya ce Faransa ba ta da niyyar aikewa da sojojinta domin yaki da masu kishin Islama da yanzu haka ke ci gaba yakar dakarun gwamnatin kasar.

Talla

A lokacin ziyarar ne dai minista Laurent Fabius ya yi amfani da wannan dama domin raba wa mazauna yankin da ke fama da rikici kayayyakin jinkai, kuma a lokacin ne ya bayyana cewa Faransa ba ta da niyyar aikewa da sojoji domin yaki da ‘yan bindigar, to sai dai duka haka kasar za ta ci gaba da taimaka wa tsirarru a cikin kabilu ko mabiya addinai da ke fuskantar barazana daga ‘yan bindiga.

Faransa dai ta aike da dimbin kayayyakin jinkai ne da suka hada har da magunguna, yayin da a gefe daya mininstan na harkokin waje ya shirya ganawa da manyan jami’an kasar ta Iraki da kuma na Kurdawa.

Yanzu haka dai akwai dubban mutane ‘yan kabilar larabawan Yezidi da kuma kiristoci da ke tserewa daga garuruwansu a cikin tsaunukan Sinjar, sakamakon barazanar da suka ce suna fuskanta daga ‘yan bindigar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.