Majalisar dokokin Ukraine ta kasa gudanar da mahawara game da bukatar Tymoshenko
Majalisar dokokin kasar Ukraine ta kasa gudanar da mahawara dangane da bukatar neman bai wa tsohuwar fira ministar kasar Ioula Tymoshenko damar zuwa kasashen ketare domin jinya bayan da ta share tsawon lokaci tsare a hannun hukumomin kasar.
Wallafawa ranar:
Da farko dai an tsara majalisar za ta bayyana matsayinta dangane da wannan bukata a gaban manzon Kungiyar ta Tarayyar Turai wato yayin da da kasar ta Ukraine ke neman kara samun karbuwa a cikin kungiyar.
A ranar Alhamis ne ake sa ran majalisar kasar za ta yi mahawara akan wasu kudirori guda hudu da ke magana akan baiwa masu laifi damar fita kasashen wajen domin neman magani.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu