Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai

Faransa ta nemi a kawo karshen matsalar bakin haure a Turai

Kasar Faransa zata bukaci kungiyar kasashen Turai, ta dauki matakin kare irin matsalar da aka samu na jirgin bankin hauren da ya nitse a mashigin kasar Italia, abinda yayi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane.Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius ne ya sanar da haka, inda yake cewa ba zasu bar mashigin ruwan Mediterranean ya zama makabarta ba, saboda haka ya zama wajibi su dauki mataki akai.Fabius yace shugaba Francois Hollande zai gabatar da kudirin a taron shugabanin kasashen Turai da za’ayi ranar 24 da 25 na wannan wata.Ita ma kasar Italia ta bukaci shugabanin na Turai su duba matsalar, dan ganin an dauki matsayi na bai daya.Kasashen Italy da Faransa sun bukaci taron Ministocin cikin gidan taraiyyar ta Turai, su tattauna lamarin a taron sun a gobe talata, dan basu shawara akai, da kuma yadda za’a hukunta masu safarar bakin hauren ba bisa ka’ida ba. 

Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius.
Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius. REUTERS/Brendan McDermid
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.