Isa ga babban shafi

Tsadar garin kwaki ta janyo karuwar farashin abinci a Najeriya - NBS

Hukumar Kididdiga ta Najeriya, NBS, ta fitar da wani rahoto da ke cewa hauhawar farashin kayan abinci ya karu zuwa kashi 33.20 bisa 100, tana mai cewa garin kwaki ne ya haddasa tsadar abincin.

Garin kwaki mai launin fari da kuma ruwan dorawa a wata kasuwa da ke birnin Legas.
Garin kwaki mai launin fari da kuma ruwan dorawa a wata kasuwa da ke birnin Legas. © Premiumtimes
Talla

Rahoton na NBS ta ce hauhawar farashin kayayyaki, wanda ya kai kashi 31.70 cikin 100 a watan Fabrairu, ya nuna karuwar kashi 1.50 cikin 100.

Haka kuma, hauhawar farashin kayan abinci ya karu zuwa kashi 40 bisa 100 inda take ganin farashin garri, akpu, kankana, da dai sauransu sune kan gaba wajen karuwar kididdigar da aka samu.

NBS ta bayyana cewa, hauhawar farashin kayayyaki ya kai kashi 11.16 bisa dari idan aka kwatanta da adadin da aka samu a watan Maris na 2023, wanda ya kai kashi 22.04.

Hukumar ta lura cewa hauhawar farashin abinci a watan Maris din 2024 ya kai kashi 40.01 bisa dari adadin da ya wuce wanda ta saba gani a duk shekara.

Hauhawar farashin kayan abinci a kowace shekara ya samo asali ne sakamakon hauhawar farashin kayayyaki kamar garri, gero, dawa, doya, manja da dai sauransu, a cewar rahoton na NBS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.