Isa ga babban shafi
TSADAR RAYUWA

Najeriya: An daka wawa kan motar abinci ta kamfanin BUA a Zaria

Wasu bata gari sun kai hari kan wata motar kamfanin BUA dauke da kwalayen taliya spaghetti a kan titin Dogarawa, wato babbar hanyar Zaria zuwa Kano.

Yadda mutanen suka daka wa motar kamfanin BUA dauke da kayan abinci wawa a Zariya kenan.
Yadda mutanen suka daka wa motar kamfanin BUA dauke da kayan abinci wawa a Zariya kenan. © dailytrust
Talla

Wannan dai na zuwa ne mako guda bayan da wasu fusatattun mutane suka yi awon gaba da tirelolin da ke makare da kayan abinci a yankin Suleja da ke jihar Neja, inda suka sace buhunan shinkafa da sauran kayan abinci, daidai lokacin da ake cikin halin kunci a kasar.

Tirelolin dai an ce sun nufi Abuja ne daga Kaduna, inda ‘yan dabar suka tare hanya tare da kona tayoyi a kan titin.

Wani ganau ya bayyana wa jaridar Dailytrust cewa al’amarin na ranar Juma’a ya faru ne da misalin karfe 3:15 na rana bayan direban motar ya faka ta a gefen titi domin yin sallah.

Ya ce nan da nan bayan direban ya yi fakin, mutanen suka fara kwashe kwalayen taliyar spaghetti.

An bayyana cewa, rundunar ‘yan sandan da aka tura wurin da lamarin ya faru, ta cafke mutane biyar da ake zargi.

Bayanai sun tabbatar da cewa, babu ko da kwalin taliya guda da mutanen suka bari a cikin motar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.