Isa ga babban shafi

Tinubu ya umarci gaggauta fitar da tan dubu 200 na abinci ga 'yan Najeriya

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umurnin gaggauta fitar da tan dubu 200 na abinci daga rumbun aje abincin gwamnatin domin rabawa jama’ar kasar da nufin rage radadin cire tallafin man da ya haifar da tsadar rayuwa ga jama’a. 

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu. REUTERS - STRINGER
Talla

Har ila yau, shugaban ya kuma bada umurnin fitar da tan dubu 250 na takin zamani domin rabawa manoma tare da ingantattun iri domin tinkarar aikin noma da samar da abinci ga jama’a. 

Tinubu ya bayyana wadannan matakai ne a yau litinin lokacin da ya ke yi wa jama’ar kasar jawabi dangane da halin tsadar rayuwar da ya dabaibaye jama’a. 

Shugaban kasar ya kuma bayyana cewar gwamnatin sa ta ware naira biliyan 200 domin zuba biliyan 50-50 wajen bunkasa noman masara da shinkafa da alkama da kuma rogo a fadin kasar. 

Tinubu ya kuma ce sun ware naira biliyan 100 domin sayen motocin safa safa 3,000 da za’a raba su a kananan hukumomi 774 domin bunkasa sufurin jama’a. 

Shugaban ya ce ya na da sane da halin da jama’a su ke ciki sakamakon wadannan matakai masu tsauri da ya dauka, wadanda yin hakan ya zama wajibi domin fitar da Najeriya daga cikin duhun da ta samu kan ta. 

Tinubun ya ce ko gwamnatin da ta gabace shi ta fahimci irin illar da ke tattare da tallafin da ake zubawa a bangaren man, dalilin da a cewarsa ya sanya ta ki zuba tallafin na watan Yunin da ya gabata. 

Shugaban ya ce da akwai wata hanya mai sauki domin fitar da Najeriya daga cikin wannan yanayi da ya dauka, amma rashin haka ya sa shi daukar wadannan matakai masu tsauri yanzu, amma kuma kowa zai ci gajiyar su a nan gaba kadan. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.