Isa ga babban shafi
Najeriya

Jonathan ya kafa kwamiti don daukaka kara akan yankin Bakassi

Bayan shekaru goma da yanke hukuncin mika Yankin Bakassi ga kasar Kamaru, shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan, ya kafa kwamitin da zai bashi shawara domin daukaka kara kan hukuncin. Bayan kwashe daren jiya yana gudanar da taro tare da Shugaban Majalisar Dattawan, David Mark da shugaban Majalisar wakilai, Aminu Tambuwal, da kuma Ministan shari’a, shugaba Jonathan ya baiwa kwamitin kwanaki uku dan gudanar da aikin. 

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a lokacin da yake zatawa da kamfanin Dillacin Labaran Reuters a fadar shugaban kasa.
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a lokacin da yake zatawa da kamfanin Dillacin Labaran Reuters a fadar shugaban kasa. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Tsohon karamin Ministan Shari’a, Musa Elayo Abdullahi ne ya jagoranci tawagar Najeriya a lokacin da aka yi shari’ar shekarun da su ka gabata, inda kotun duniya ta mallakawa kasar Kamaru yankin.

Sai dai wata takaddama da taso a yanzu haka ita cewa, an gano wasu sabbin bayanai da su ka nuna cewa ainihin yankin na Bakassi na Najeriya ne.

Hakan kuma ya sa wasu suka matsa lamba cewa sai shugaba Jonathan ya daukaka kara, domin karbo yankin ya dawo Najeriya.

A yanzu haka, Najeriya, na da yanzu har zuwa Talatar mako mai zuwa, na damar ta daukaka kara, idan har ya wuce hakan bata da hurumin da za ta yi hakan saboda shekaru goma ne wa’adin rufe daukaka karar da kotun ta duniya ta yanke.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.