Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: An kafa dokar hana fita a garin Mubi

Gwamnatin Jihar Adamawa dake Nigeria, ta kafa dokar hana fita a garin Mubi, saboda kisan da aka yiwa mutane 26 a garin, akasarin su daliban babbar Kwalejin Fasaha ta Gwamnatin Tarayya. Tuni dai aka rufe makarantar, kuma rahotanni sun ce kisan ya jefa fargaba ga daukacin mutanen garin. Rundunar ‘Yan Sanda da sauran jami'an tsaro a jihar Adamawa dake Nigeria sun kaddamar da farautar wasu mutane da suka kashe dalibai 26 yau da safe a garin Mubi.  

Jami'an tsaro a lokacin dokar hana fita a wata Jihar Najeriya
Jami'an tsaro a lokacin dokar hana fita a wata Jihar Najeriya sphotos-a.xx.fbcdn.net
Talla

Daliban na karatu ne a Makarantar koyon Sana'oi da ake kira Federal Polytechnic Mubi.
Bayanai na nuna maharan sun bi gida-gida ne da daliban ke zama, suna kiran sunayen daliban daya- bayan-daya suna kashewa.
 

Kakakin Rundunar 'Yan sandan jihar Adamawa, DSP Mohammed Ibrahim ya gaskata aukuwan wannan al'amari, bayan ya ziyarci inda lamarin ya auku tare da sauran jamian tsaro dake jihar.
 

Maimagana da yawun Hukumar bada agajin gaggawa ta Tarayya y ace rahotanni sun nuna cewa, daliban da aka kashe ‘Yan takara ne a wani zabe da aka gudanar a kwalejin.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.