Isa ga babban shafi
Najeriya

‘Yan fashin teku sun kwace wani jirgin ruwan Singapore a Najeriya

Wasu ‘Yan fashin teku, sun kwace wani jirgin ruwan kasar Singapore, a Jihar Legas, da ke kudancin Najeriya.Wannan fashi, shine na biyu da ya auku a cikin sati biyu da su ka wuce akan gabar Tekun Guinea, a cewar Hukumar mai ta Kasa da Kasa mai kula da Teku.  

Taswirar gabar Tekun Guinea
Taswirar gabar Tekun Guinea Wikipedia
Talla

Jirgin, a cewar hukumomi a birnin Kuala Lumpur, jirgin wanda na mai ne, na dauke da ma’aikata 23 a cikinsa.

Koda yake, hukumomin basu bad a bayanai akan yadda ‘Yan fashin tekun su ka kwace jirgin ba.

Sai dai shugaban hukumar, Noel Choong, ya ce sun sanar da hukumomin da su ka dace, kuma sun a yin wani abu akai.

Choong ya kara da cewa “mu damuwar mu a yanzu, shi ne tsaron lafiyar ma’aikatan wadanda su ka kulle kansu a wani daki, da kuma yawan kwace jirage da ake yi a teku”.

A watan da ya gabata, ‘Yan fashin tekun, sun kwace wasu jirage biyu a yankin Togo wadanda ke dauke makil da mai, inda su ka kwashe man bayan sun kwace jiragen, wanda daga baya kuma aka sako jiragen tare da duk ma’aikatan.

A fadar Choong, wadanda su ka aikata wannan fashin sun e su ka kwace jirgin na Singapore, inda ya kara da cewa, “ yadda su ke yi, shine sai su je su juye man a wani jirgi su kuma yi wa jirgin kankat sannan sai su sake shi duk a cikin kwanaki biyar.”

Hukumar ta kasa da kasa mai kula tekun ta sha yi wa jirage gargadi da su yi hattara a duk lokacin da su ke tafiya a kan gabar tekun yammacin Afrika, su kuma, jawo hankalin hukuma a duk lokacin da su ka fuskanci wata barazana.

An kai hare hare akalla sau 37 da su ka hada da kwace jirage, yin garkuwa, kisa aw wannan shekara, a yankin na gabar tekun Guinea.

‘Yan fashin dai su kan kwace jirage daukan kaya ne, musamman mai, inda su ke juye kayan a jirginsu su je su sayar a kasuwar bayan fage.

Kasashen Najeriya da makwabaciyarta, ta Jamhuriyar Benin sun taba gudanar da wani shawagi a shekarar da ta gabata, a yunkurinsu na ganin cewa an magance matsalar fashin jirage.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.