Isa ga babban shafi

Haaland ya zura kwallaye 5 rigis a ragar Luton a ci gaba da gasar FA

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester city Erling Haaland ya yiwa ragar Luton ruwan kwallaye a gasar cin kofin FA da ake gudanarwa

Erling Haaland da wasan kungiyar Manchester City.
Erling Haaland da wasan kungiyar Manchester City. © AFP - DARREN STAPLES
Talla

Kungiyoyin biyu sun kara da juna ne a wasan gab dana kusa dana karshe, inda shi Haaland din ya zura kwallaye 5 cikin shida da kungiyar sa ta ci Luton din.

Wannan shine karo na 8 da dan wasan dan asalin kasar Norway ke cin kwallo daga uku zuwa sama, yayin da ya zama dan kwallo mafi hazaka sau biyu a jere a wasannin da kungiyar ta buga.

City din ce dai ta bude nasarar da cin farko a minti na 4 da take wasan ta hannun dan wasanta Haaland bayan da Kevin de Bruyne ya mika masa kwallon.

Bayan minti 15 da cin wannan kwallo, zakakuran yan wasan suka kuma hada kai suka afkawa ragar Luton din.

Kafin tafiya hutun rabin lokaci kuma dan wasan kungiyar Luton din Jordan Clark ya ragewa kungiyar sa kwallo daya daga bugun kusurwa, yayin da Rob Erdwards ya warware kwallo ta biyu, inda aka je hutun rabin lokaci ana kwallo 2-2.

Bayan dawowa hutun rabin lokacin ne kuma City din ta rika ragargazar ragar Luton har sai da ta zura mata karin kwallo hudu, uku daga cikin su ta hannun Haaland, lamarin da ya cike kwallo biyar a wasa daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.