Isa ga babban shafi
Faransa

Kotun Faransa ta hukunta Bafaranshe saboda Jihadi a Mali

Wata kotun daukaka kara a kasar Faransa ta yankewa wani bafaranshe hukuncin zama a gidan yari har na tsawon shekaru shida, sakamakon samun sa da laifin yunkurin agazawa Mayakan Jihadi a Kassr Mali

Mayakan Jihadi
Mayakan Jihadi
Talla

A Shekara ta 2012 ne, aka kama Bafaranshen mai asali a Mali, Ibrahim Ouattara a tsakiyar kasar ta Mali, a daidai lokacin da yake yunkurin shiga kungiyar Mujahidan, da suka mamaye arewacin Kasar.

A lokacin sauraren karar, Ouattara mai shekaru 27 cewa yayi, daukan makamai a fafutukar kare muradi ba aibi bane, yayinda ya jadda kudirinsa na  cigaba da kasancewa a wannan turbar.

A farko dai kotun data tuhumi Ouattara a watan Yulin bara, ta yanke masa hukuncin zama gidan kaso na shekaru hudu, amma daga bisani masu shigar da kara na Gwamnati suka bukaci karin shekaru biyu.

Tun yana dan shekara 16 ne, Ouattara ya koma addinin Musulunci yayinda ya gamsu da manufar Jihadi ta hanyar bincike a Yanar gizo.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.