Isa ga babban shafi
Libya

Mayakan IS sun kafa sansani a Libya

Wani babban Jami’n tsaron Amurka yace Kungiyar IS da ke da’awar Jihadi a Iraqi da Syria ta kafa wani sansanin da ta ke horar da mayaka a gabacin kasar Libya. tuni kasashen yammaci suka bayyana fargabar cewa Mayakan na iya samun wuri a Libya saboda rikicin da kasar ke fama da shi.

Wani Sojan Kurdawa rike da makami a wani tsauni kusa da yankin Khazir da ke kusa da Mosul inda Mayakan IS suka kwace iko a Iraqi
Wani Sojan Kurdawa rike da makami a wani tsauni kusa da yankin Khazir da ke kusa da Mosul inda Mayakan IS suka kwace iko a Iraqi REUTERS/Ahmed Jadallah
Talla

Janar David Rodriguez kwamandan kula da tsaro a Afrika yace daruruwan mayakan IS ne ake horarwa a sansanin, amma ya yi watsi da daukar matakin soji a yanzu.

Shugaban Kasar Faransa Francois Hollande ya bayyana cewar a shirye ya ke ya kara kaimin hare haren da kasar ke kai wa kan mayakan IS da ke ikon wasu yankuna a Iraqi da Syria.

Wata sanarwa hadin guiwa da shugaban ya bayar tare da Firaministan Iraqi Haider al Abadi, ta nuna cewar Faransa za ta ci gaba da bayar da gudumawar soji ga Iraqi da ke fuskantar matsalar ayyukan ta’adanci.

Al abadi ya kuma bayyana cewar ana samun nasarar yakin domin sun kusa kakkabe kasar daga hannun yan ta’addan.

Tuni dai Amurka ta kaddamar da yaki kan Mayakan IS a Iraqi da Syria.

Tun kawar da gwamnatin Kanal Ghaddafi kasar Libya ke fama da matsalar tsaro, kuma shugaban IS Abu Bakr al Baghdadi ya bayyana goyon bayansa ga mayakan Libya da ke da’awa a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.